Zafin rana yayin aikin hajji a Saudiyya
June 13, 2024Masu lura da al'amuran yau da kullum sun nunar da cewa matakan rage tsananin zafin ba za su wadatar ba, matukar kasa mai tsarkin ba ta sauya manufofin yaki da sauyin yanyi na dogon lokaci ba. Aikin Hajjin na bana da ke farawa a ranar 14 ga wannan watan na Yuni da muke ciki, ba wai kawai zai zama sauke farali ne ga Musulmi kusan miliyan biyu da suka fito daga kasashe kusan 180 ba zai zama kalubale na kiwon lafiya saboda yanayin zafin rana da ya karu fiye da kima. Shugaban cibiyar nazarin yanayi na kasar Saudiyya Ayman Ghulam ya ce yanayin zafi da ake sa ran samu a aikin Hajji a bana, zai karu da digiri sama da digiri daya zuwa biyu a ma'aunin Celsius a Makkah da Madina, idan aka kwatanta da yadda aka saba samu.
Karin Bayani: Matsin arziki na barazana ga Hajjin 'yan Najeriya
Akwai ma yiwuwaMatsin arziki na barazana ga Hajjin 'yan Najeriyar samun zafin da ya kai digiri 44 zuwa 50 a ma'aunin Celsius a birnin Makkah, amma kamar yadda hukumomin Saudiyya suka yi alkawari an ninka cibiyoyin samar da ruwan sha a babban masallacin Makkah tare da sanya na'urorin sanyaya daki a harabar manyan masallatan domin maniyata su samu sa'ida. Hajiya Aisha da ta fito daga Jamhuriyar Nijar ta ce duk da ta saba da yanayin zafi saboda kasarta ta asali na fuskantar kwararowar Hamada, zafin da ta ji a Madina ya kai makura. Duk da wannan zafin ranar, maniyata aikin Hajji za su shafe tsawon sa'o'i 30 a wuraren da babu inuwa da AC ciki har da tsayawa a dutsen Arafat na yini guda tsakanin ketowar alfijir da faduwar rana, da zirga-zirga ta sa'o'i da yawa a gefen Makkah na wasu kwanaki. Saboda haka, gajiya da kishirwa na daga cikin manyan haduran da ke tattare da aikin hajjin a bana.
Ko da a shekara ta 2023 da ta gabata zafin rana ya kai digiri 48, lamarin da ya sa kusan mahajjata dubu takwas da 400 ga kwanciya a asibiti sakamakon matsanancin zafin. Wani bincike da aka fitar a mujallar likitanci ta Journal of Travel Medecine, ya bayyana cewa mahajjata da suka fito daga kasashen da ba a zafi sosai kamar Turai sun fi fuskantar hadarin rasa rayukansu sakamakon zafi fiye da mutanen da suka saba da irin wannan yanayi na zafi. Dakta Abubakar shi ne shugaba tawagar liktioci a Hukumar Alhazai ta Najeriya, ya bai wa mahajatta shawarwari kan hanyoyin magance tsananin zafin ranar da ake fuskanta. Koda yake, karuwar yanayin zafin ba wai kawai alhazai yake jefawa cikin hatsari ba. Wani bincike da jami'ar kimiyya da fasaha ta Sarki Abdallah ta kasar Saudiyyan ta gudanar, ya tabbatar da cewa yanayin zafi ya karu da kasa digo hudu a kowadanne shekaru 10 a cikin shekaru 40 din da suka gabata.
Karin Bayani: Alhazai na tsaka da kololuwar aikin Hajji
Tobias Zumbrägel da ke bincike a sashen nazarin yanayin dan Adam na jami'ar Heidelberg da ke Jamus, ya ce "Hasashe da yawa na nuna cewar wasu sassa na kasar Saudiyya za su iya zama wadanda ba a iya rayuwa a cikinsu a karshen wannan karni". Masanin ya ci gaba da cewa, ana sa ran samun guguwa mi karfi da tumbatsar teku da kuma karancin ruwa a yankin da ya riga ya kasance hamada. Ita dai Saudiyya, ta kuduri aniyar sauya sheka zuwa samar da makamashin da ba ya gurbata muhalli a nan gaba. Amma a daya hannun, tana ci gaba da kasancewa a sahun gaba wajen fitar da mai a duniya. Sai dai masana sun ce akwai bukatar kasar ta mayar da hankali kan shirin kasa da kasa na yaki da sauyin yanayi, tare da gudanar da tarin bincike domin gano hanyoyin kare yawan al'umma da kuma mahajjata daga zafin rana da ke da nasaba da sauyin yanayi.