1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Najeriya: Saukin farashin kayan abinci

August 15, 2024

Bayan share tsawon lokaci cikin halin tsanani, Tarayyar Najeriya na kallon raguwar hauhawar farashin abinci da ma ragowar bukatun rayuwa cikin kasar.

https://p.dw.com/p/4jW9d
Najeriya | Bola Tinubu | Zanga-zanga | Tsadar Rayuwa
Shugaban Najeriya Bola Ahmed TinubuHoto: Sunday Aghaeze/Nigeria State House via AP/picture alliance

Wata sabuwar kididdiga dai ta ce, a karon farko cikin watanni 19 hauhawar farashi na nuna alamun raguwa cikin kasar. Kuma daga kaso 34 da digo biyu da kasar ta gani a watan Yuni tashin farashin ya ragu zuwa kaso 33 da digo uku a cikin watan Yuli na jiya, a wani abun da ke zaman alamun sauki kan tasirin zare tallafin man fetur da kila ma rushewar darajar Naira a kasar. Kaka cikin batu na abinci ne dai ake ta'allakawa da ragin, wanda ga dukkan alamu ke shirin sanyaya zuciya cikin kasar da ke ji a jiki. Mubarak Hussaini dai na zaman wani dillalli na cimakar a kasuwar dei-dei da ke Abuja fadar gwamnatin kasar, kuma ya ce ana ganin rushewar farashi a cikin wasu nau'o'in abincin. Hauhawar farashin dai, na zaman ta kan gaba cikin rikicin da ya mamaye kasar a farkon wannan wata na Agusta. Abujar dai na fatan saukar farashin da ke iya koma wa ya zuwa kaso 27 cikin 100 ya zuwa karshen shekarar bana, sakamakon wasu jerin matakai da suka hada da bayar damar shigar da abinci cikin kasar a karon farko cikin lokaci mai nisa.

Najeriya | Tsadar Rayuwa | Yunwa | Bola Ahmed Tinubu | Zanen Barkwanci
Yunwa da tsadar rayuwa sun addabi 'yan NajeriyaHoto: DW

To sai dai kuma murnar na zaman gajeruwa, a tunanin Dakta Isa Abdullahi da ke zaman kwararre ga tattalin arziki da kuma ya ce matakai na masu mulki na kasar sun yi kadan. Koda yake a yayin da masu mulkin ke hango sauki daga kaka, har yanzu jiga-jigan hauhawa ta farashin na shawagi cikin kasar. A cewar Abubakar Aliyu da ke sharhi ga tattali na arzikin ke, akwai alamun jan aikin da ke gaban 'yan mulkin Tarayyar ta Najeriya a halin yanzu. Shi kansa wani shirin shigo da abincin da nufin rage radadi na hauhawa ta farashin na neman fadawa rikici, a yayin da kananan masu sarrafa shinkafa ke zargin gwamnatin kasar da kokarin ware su a cikin neman sauki. Akalla mutane 13 ne dai masu mulki na kasar suka tabbatar da asarar ransu, a cikin zanga-zangar neman kare yunwar da ta kwashe kwanaki har 10 cikin ana gudanar ta a Tarayyar Najeriyar.