A cikin shirin za ji Kotun hukunta manyan laifuka ta kasa da kasa ta ICC ta ba da izinin soma bincike kan kashe-kashe da sauran nau'i na cin zazafin dan Adam da suka wakana a kasar Burundi. A jamhuriyar Nijar kuma yau take ranar zagayowar shekaru 30 da rasuwar tsohon shugaban mulkin sojan kasar Janar Seini Koutche.