Harshen Hausa na fuskantar kalubale na zamani
June 30, 2020Harshe ko yare yana dorewa ne matukar masu yaren na wallafa shi ta hanyar gudanar da rubuce-rubuce bisa ka'idarsa. Kasancewa hakan ne zai ba da dama ga 'yan baya su fahimci yaren. Harshen Hausa yana daya daga cikin yaren da yake da yawan masu magana da shi musamman ma a yankin kasashen Afirka ta Yamma. Najeriya kuma ta kasance inda Hausawan suka fi yawa, sannan kuma akwai marubuta na harshen da dama. Sai dai yawan kallo da sauraro na kafofi na iya zama babbar barazana ga Hausar a cewar masana.
Rubuce-rubuce na zaman tubali na raya harshe sai dai zamani ya kawo sauyi
A Jihar Bauchi akwai wani shahararren marubucin wanda ya rubuta littattafai da dama domin bunkasawa da raya harshen na Hausa. A shekarun baya ana iya cewa rubuce-rubuce suna da matukar tasiri a tsakanin al'umma domin kuwa magabata a wancan zamanin ba su dauki lamarin da wasa ba kasancewar a kan dora manyan gobe bisa turbar karance-karance wanda hakan ke sa su taso cikin sha'awar karatu sosai. Sai dai kuma sannu a hankali zamani ya sauya, inda kallo da sauraro suka shigo kuma suka yi matukar tasiri a kan al'ummar Hausawa wanda hakan kuma ya zamo babban kalubale ga marubuta, domin kuwa wadannan abubuwa biyu sun kawo koma baya ga dabi'ar karance-karance a kasar Hausa.