Gangami gabanin taron MDD kan canji yanayi
September 20, 2019Kungiyoyi dabam-dabam mafi yawansu na matasa maza da mata da suka hadar da dalibai da masu rajin kare muhalli ne suka hallara a dandalin 'yancin na Unity Fountain, domin bin sahun wannan tattaki da ake yi a kusan daukacin kasashen duniya, domin yaki da sauyi ko dumamar yanayi wato Fridays for future. Ibrahim Yunusa matashi ne daga kungiyar CITAD, ya ce sun bar ayyukansu domin gudanar da zanga-zangar da za ta nuna yadda suka damu da halin da duniya ke ciki dangane da sauyin yanayin.
Akwai dai mata da dama da kusan za a iya cewa sun kamo yawan mazan, a wannan gangami wadanda suma suka halarci gangamin domin nuna damuwarsu kan sauyin yanayin. Rashida Hassan na daya daga cikinsu da ta fito daga kungiyar Arise ta ce sun ga haza ne ya sanya dole suka fito. Kokarin da suka yi na yin tattaki zuwa majalisar dokokin Najeriyar domin mika bukatunsu ya ci tura, domin 'yan sanda sun zagaye dandalin 'yancin na Unity Fountain, a wani mataki na tabbatar da tsaro. A yayinda matasan ke nuna damuwa a kan lamarin, har zuwa kammala wannana taro, babu wani jami'in gwamnati da ya kasance a wurin da nufin mayar da martani a kan kiran da matasan da masu rajin kare muhallin ke yi na a dauki matakin.