1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW
Salon rayuwa

Sauyin yanayi na haifar da rikice-rikice

Eyong Blaise LMJ/SB/AH
October 31, 2023

Sauyin yanayi ya tilasta mutane da dama a yanking Arewa mai Nisa na Kamaru kauracewa gidajensu. A shekaru biyun da suka gabata kuma, rikici kan samar da ruwa ya tilasta dubbai barin gidaje.

https://p.dw.com/p/4YFLY
DW I Sauyin yanayi na tilasta mutane gudun hijira
Sauyin yanayi na tilasta mutane gudun hijiraHoto: DW

Sauyi ko dumamar yanayi, ya tilasta mutane da dama a yanking Arewa mai Nisa na Kamaru kauracewa gidajensu. A shekaru biyun da suka gabata kuma, rikici kan samar da ruwa ya tilasta dubbai barin gidajensu. Wani rahoto na Hukumar Kula da ‘Yan Gudun Hijira ta Majalisar Dinkin Duniya UNCHR, ya nunar da cewa wadannan rigingimu sun yi sanadiyyar mutuwar kimanin mutane 50 baya ga kona kauyuka da dama a yankin.

Karin Bayani: Bamenda: Dokar zaman gida na hada zumunci

'Yan gudun hijira na Kamaru
'Yan gudun hijira na KamaruHoto: Pius Utomi Ekpei/AFP/Getty Images

Rikici tsakanin masunta da manoma da kuma makiyaya ya kazanta a Kamaru, inda kimanin mutane dubu 10 suka tsere zuwa makwabciyar kasa Chadi kana wasu dubu 15 suke warwatse a cikin kasar a sansanonin ‘yan gudun hijira. Ahmed Bouba makiyayi ne da ke kiwon shanunsa a kusa da kauyen Bogo. A cewarsa bai san yadda zai yi ba, ganin cewa lokacin bazara ya fara da wuri a bana. Hakan dai ya sanya matsalar da yankin ya saba samu duk shekara, ta ta'azzara. Bouba ya nunar da cewa, a shekarun baya-bayan nan yanayi ba shi da tabbas. A cewarsa imma a samu tsananin zafi ko fari, ko kuma yanayin marka-marka.

Matsalar rashin ruwan dai, ta zama silar afkuwar rikici. Kimanin 'yan gudun hijira 5,000 ke zaune a wannan sansanin, kuma Salli Sakim na daga cikin wadanda rikicin manoma da masunta da kuma makiyaya a daya bangaren ya tilasta musu yin kaura.  

Mutane sun samu mafaka, sai dai gagarumin kalubalen sauyi ko dumamar yanayi da yankin ke ci gaba da fuskanta lokaci kawai suke jira kafin tilas su sauya sheka. Kawo yanzu dai gwamnati ba ta sanar da bayar da wani tallafin a zo a gani ga mutanen da ke sansanin 'yan gudun hijirar ba. Mutane da dama a nan na fafutukar abin da za su ci, kuma ga dukkan alamu wannan shi ne farkon yanayin bazara mafi tsayi da aka shiga a kasar.