1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW
SiyasaJamus

Scholz ya ce Jamus na bukatar 'yan cirani

Abdullahi Tanko Bala
September 11, 2024

Shugaban gwamnatin Jamus Olaf Scholz ya kare manufar gwamnatinsa a wani jawabi da ya yi a majalisar dokoki inda ya jaddada bukatar daukar kwararrun ma'aikata daga waje.

https://p.dw.com/p/4kW9l
Shugaban gwamnatin Jamus Olaf Scholz
Shugaban gwamnatin Jamus Olaf ScholzHoto: Ebrahim Noroozi/AP Photo/picture alliance

Scholz ya ce babu wata kasa a duniya mai karancin ma'aikata da tattalin arzikinta zai bunkasa.

Shugaban gwamnatin na Jamus ya baiyana wa majalisar ta Bundestag cewa wannan shi ne gaskiyar lamari kuma dole a fuskanci hakan.

Jawabin nasa na zuwa ne yayin da ake tsakiyar zazzafar muhawara a Berlin kan manufofin cirani da yan gudun hijira.

A ranar talata talata tattaunawa ta ci tura tsakanin kawancen gwamnatin Scholz da 'yan ra'ayin rikau ba tare da cimma wata matsaya ba.