1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW
SiyasaAfirka

Senegal: Shugaba Sall ya dage zabe

February 3, 2024

Shugaban Senegal Macky Sall ya sanar da jingine babban zaben shugaban kasa da aka shirya gudanarwa a ranar 25 ga watan na Fabrairu 2024, a kasar da ta kafa tarihi wajen gudanar da zabe mai inganci a Afrika.

https://p.dw.com/p/4c19d
Shugaban Senegal Macky Sall
Shugaban Senegal Macky Sall Hoto: Seyllou/AFP

Shugaba Macky Sall ya ce wasu daga cikin dalilan da ya sanya gwamnati daga zaben sun hadar da batun takaddamar da ta kunno kai kan tantance 'yan takara da zargin cin hanci da rashawa da ya dabai-baye ayyukan hukumar zaben.

Shugaba Sall, ya dauki wannan mataki ne bisa dogaro ga kundin tsarin mulkin kasar da ya ba shi damar dage zaben, a daidai lokacin da aka kaddamar da yakin neman zabe a fadin kasar a hukumance, duk da cewa bai sanar da ranar da za a gudanar da zaben ba.

Kazalika, shugaban da ba zai sake tsayawa takara ba, ya ce 20 daga cikin 'yan takarar na da shaidar kasancewa 'yan wasu kasashen wanda hakan ya ci karo da kundin tsarin mulkin Senegal.

Senegal na daga cikin kasashen Afrika da suka yi fice wajen tabbatar da tsarin dimukradiyya mai inganci kuma abin kwatance a tsakanin sauran da guguwar juyin mulki ke ci gaba da kadawa a wasu sassan yammacin Afrika.