Senegal: 'Yan adawa sun bakaci a saki dan takararsu
February 18, 2024A cikin wata sanarwa da suka fidda a ranar Lahadi 18.02.2024, 'yan adawan sun ce dole ne a samar da daidaito a tsakanin dukannin 'yan takaran da ke zawarcin kujerar shugaban kasa kamar yadda kundin tsarin mulkin kasar ya tanadar.
Karin bayani: Senegal: 'Yan adawa sun yi zanga-zanga cikin lumana
Kazalika 'yan adawan sun kuma bukaci da a saki madugunsu Ousman Sonko wanda aka daure a watan Yulin shekarar da ta gabata bisa yanke masa hukunci kan zargin tada zaune tsaye da hada baki wajen aikata muggan laifuka da kuma wasu tuhume-tuhume da ya musanta.
Tun bayan barkewar boren adawa da matakin dage zabe, gwamnatin Macky Sall ta sallami 'yan adawa da dama daga gidan yari da nufin kwantar da guguwar siyasar ta kada a kasar sai dai har yanzu ana ci gaba da tsare wadansu.