Shaci-fadi da fargaba game da cutar Ebola
January 14, 2015Shaci-fadi da Fargaba game da cutar Ebola
Fargaba da shaci fadi da maganganu marasa tushe balle makama na daga cikin abubuwan da suka yi sanadin bazuwar annobar Ebola a yammacin Afrika.
Shaci-fadi : Idan na hadu da wanda ke dauke da cutar Ebola zan kamu da ita nan take.
Ansa: Ba a kamuwa da Ebola da zarar an hadu da wanda ke dauke da ita don cutar ba ta yaduwa ta iska. Ana yada ta ne kawai ta hanyar taba ruwan da ke fita daga kafofin jikin mutumin da ke dauke da kwayar cutar.
Shaci-fadi: Ba za a iya yin nasara wajen yakar cutar Ebola ba.
Ansa: Kwararru sun yi imanin cewar za a iya yakar cutar idan kasashen duniya suka hada karfi da karfe ko da dai hakan kan iya daukar watanni kafin a kai ga ci. Ana kokarin samar da magungunan rigakafin cutar kuma nan gaba ne za a fara amfani da su.
Shaci-fadi: Kasashen yamma ne suka kirkiro Ebola
Ansa: Babu wata hujja da za a iya yin amfani da ita wajen nuna cewar kasashen yamma ne suka kirkiro Ebola. Turawan yamma ne suka fara gano cutar a shekara ta 1976 amma masu bincike sun ce dama akwai kwayar cutar tun ma kafin wannan lokaci a dazukan da ke tsakiyar Afrika da kudu maso gabashin nahiyar Asiya.
Shaci-fadi: Za a iya warkar da Ebola
Ansa: Ya zuwa yanzu babu babu wani magani da aka amince da shi a matsayin wanda zai warkar da Ebola. Za dai a iya magance ta, ta bin wasu hanyoyi na daban. A yanzu dai ana cigaba da gwaji kan magungunan kashe kwayoyin cutar. Masu magungunan gargajiya da dama sun ce suna warkar da Ebola amma hanyoyin da suke bi na da hadarin gaske. Kimanin mutane 400 ne suka rasu a Saliyo lokacin da wata mai magani ta ce ta warkar da cutar. Maimakon magance cutar sai ta buge da kara yada cutar.