1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW
Salon rayuwaJamus

Bikin tunawa da hadewar Jamus karo na 33

Lateefa Mustapha Ja'afar Jung, Marina
October 3, 2023

Wani sabon littafin tarihi da aka fitar a makarantun kasar Rasha mai suna Medinsky Book, ya sake bayyana Jamus a matsayin wani bangaren na Jamus ta Gabas ko kuma DDR gabanin sake hadewar Jamus da Gabas da ta Yamma

https://p.dw.com/p/4X4gU
Birnin Berlin | Jamus | Ranar hadewar Jamus ta Gabs da ta Yamma
Birnin Berlin | Jamus | Ranar hadewar Jamus ta Gabs da ta YammaHoto: Fabian Sommer/picture alliance

Shekaru 33 ke nan da sake hadewar Jamus a matsayin dunkulalliyar kasa, inda Jamus ta Gabas ko kuma DDR da Jamus ta Yamma suka sake hadewar a ranar uku ga watan Oktobar 1990. Shekaru 45 bayan kawo karshen yakin duniya na biyu, Jamus ta sake zama kasa daya al'umma daya. Wannan tarihin na Jamus dai, ba za a iya raba shi da Tsohuwar Tarayyar Soviet da kuma jagoran jam'iyyarta ta gurguzu wato Mikhail Gorbachev ba. Masana tarihi, sun jima suna tattauna rawa dabam-dabam da Gorbachev ya taka a Jamus da Rasha. 

Littafin tarihin na 'yan makarantar sakandare da aka wallafa a watan Satumbar da ya gabata wato Medinsky Book dai, tshon ministan al'adun Rasha kana mashawarci ga Shugaba Vladimir Putin wato Vladimir Medinsky da kuma shugaban Cibiyar Nazarin Huldar Kasa da Kasa ta Moscow Anatoly Torkunov ne mawallafansa. Matakin Rasha na ayyana Jamus a matsayin wani bangare na DDR na baya-bayan nan, ya harzuka masana tarihin Jamus da dama. Da yake bayyana ra'ayinsa kan sabon littafin tarihin, shugaban kungiyar malaman tarihi ta kasa a Jamus Niko Lamprecht cewa ya yi

Karin Bayani:  Shekaru 30 da faduwar katangar Berlin

"Wannan wani babban sabon salo ne na sake fassara tarihi, Shugaba Vladmir Putin ya jima yana irin wannan a fannoni dabam-dabam tsawon sama da shekaru 20 din da suka gabata. A yanzu abin takaicin shi ne, Putin ya sake rubuta tarihi. A ganinsa, Tarayyar Rasha na da duk wata dama da za ta iya dawo da wasu abubuwa gareta."

Birnin Berlin | Jamus | Ranar hadewar Jamus ta Gabs da ta Yamma
Birnin Berlin | Jamus | Ranar hadewar Jamus ta Gabs da ta YammaHoto: Jörg Schmitt/dpa/picture alliance

Bayan kammala yakin duniya na biyu ne, kasashen Amurka da Tsohuwar Tarayyar Soviet da Birtaniya da kuma Faransa suka yi rabon ganima da Jamus. Sun gaza samo mafita ga Jamus, inda aka kasafta kasar zuwa Jamus ta Yamma da ta Gabas. Jamus ta Gabas ko kuma DDR ta fada karkashin ikon Tsohuwar Tarayar Soviet, inda Berlin ta zama cibiyar yakin cacar baka. DDR ta kwashe sama da shekaru 40 kafin a shekara ta 1989 a gudanar da zanga-zangar da ake wa lakabi da juyin-juya halin zaman lafiya, inda a ranar tara ga watan Nuwamba na 1989 din aka rusa bangon Berlin da ya raba Jamus ta Gabas din wato DDR ta Jamus ta Yamma.

Daga faduwar bangon zuwa ga zaben farko a 1990 a DDR da kuma sanya hannu kan yarjejeniyar da aka yi wa lakabi da "Two-Plus-Four Treaty", sune suka share hanyar sake hadewar Jamus ta Gabas da ta Yamma a ranar uku ga watan Oktobar 1990. Shin ya al'ummar Jamus suka karbi batun sake hadewar kasar guri guda? Shugaban kungiyar malaman tarihi ta kasa a Jamus Niko Lamprecht  ya yi karin haske yana mai cewa

Karin Bayani:  Shekaru 29 da hadewar Jamus ta Yamma da ta Gabas

"Ba a taba samun rinjaye a bangaren adawa da sake hadewar kasar ba, sai dai rinjayen masu nuna goyon baya. A watan Oktobar 1990 babu tankokin yakin Jamus da suka mamaye yankin, al'amura sun sauya baki daya ba yadda aka tsammata ba."

Sai dai Lamprecht ya ce, gabanin sake hadewar Jamus waje guda an samu mabambantan ra'ayoyi. Akwai wani mummunan kalami da 'yan siyasar Jamus suka rinka yi, wato batun cewa Jamus ta Gabas na karkashin ikon Tsohuwar Tarayyar Soviet. A cewarsa Putin ya sake fassara tarihi ne, bisa rahotanni karya da suke da asali a siyasance.

Taswirar Jamus ta Gabas da Jamus ta Yamma
Taswirar Jamus ta Gabas da Jamus ta Yamma

Rahotanni sun nunar da cewa, har zuwa baya-bayan nan ana amfani da littattafan tarhi dabam a Rasha. A 2021 littafin tarihin da ake amfani da shi a kasar, ya danganci abin da ke da nasaba da juyin-juya halin zaman lafiya ne. Sai dai daga ranar daya ga watan Satumbar da ya gabata,  littafin Medinsky ya sauya komai.