Shekau: Inanan da lafiya ta
May 5, 2017Talla
A cikin wannan makon ne dai kakakin rundunar sojojin Najeriya Birgediya Janar Usman Kuka Sheka, ya sanar cewa akwai yuwar rundanar sojojin sun raunata wasu jiga-jigagan kungiyar Boko Haram, a wasu harare-hare ta sama da sojojin suka kai kauyen Balla da ke kusa da dajin Sambisa a jihar Borno.
To sai dai sabon bidoyon ya nuna Shekau zaune a tsakiyar wasu kwamandojinsa biyu, inda ya ke cewa yana nan lafiya lau, kuma ba wanda aka raunata a cikin mukarrabansa. Kawo yanzu dai ba bu tabbacin inda aka nadi sabon bidiyon, to amma Shekau ya yi bayanin cewa a jiya Alhamis ne ya yi jawabin nasa. Amma babu martani daga bangaren jami'an tsaro kan wannan sabon bidiyo.