Jamus: Kokarin kafa gwamnatin hadaka
September 30, 2021Su dai jam'iyyun na SPD da CDU da abokiyar tagwaiotakarta ta CSU, sun kasance a matsayi na daya da na biyu a zaben 'yan majalisar dokokin ta Jamus wato Bundestag. Jam'iyyar SPD ce dai ke kan gaba yayin da CDU/CSU din ke bi mata a ,matsayi na biyu. Jam'iyyar The Greens ta masu rajin kare muhalli ce a matsyi na uku yayin da ita kuma jam'iyyar FDP ke a matsayi na hudu.
Yayin da jam'iyyar SPD ta shugaban kasar ta Jamus Frank-Walter Steinmeier da ke kan gaba a zaben, ke zawarcin jam'iyyun biyu domin kafa gwamnatin hadaka, a hannu guda jam'iyyar CDU/CSU ta shugabar gwamnati mai barin gado Angela Merkel ta bayyana cewa ita ma fa za ta iya kafa gwamnatin hadaka, inda itan ma ke zawarcin wadannan jam'iyyu biyu na The Greens da kuma FDP. Wanna dai shi ne karon farko a tsayon shekaru da gwamnatin hadakar ka iya kunsar jam'iyyu sabon zubi, maimakon SPD da C DU/CSU da aka saba da su.