A cikin shirin za a ji cewa adadin 'yan siyasar da ke shirin tunkarar kotun sauraren korafe-korafe zabukan da suka gabata a Najeriya sun kai 324. Masana da masu sharhi a Najeriya sun fara martani kan matakin hukumar NBC mai kula da kafafen yada labarai bayan da ta ci tarar wasu kafafen yada labaran kasar biyo bayan korafin 'yan siyasa.