A cikin shirin za a ji cewa, hukumomi a jihar Katsinan Najeriya sun tabbatar da sace dalibai mata a jami'ar gwamnatin tarayya da ke Dutsamma. A Jamhuriyar Nijar kawancen kungiyoyin fafutuka na M62 ce ta shigar da karar tsohon shugaban kasar, Mahamadou Issoufou kan zargin laifukan cin zarafin bil'Adama.