A cikin shirin za a ji cewa wasu kungiyoyin fararen hula masu yaki da cin hanci da rashuwa ciki har da Rotab da Tournon La Page a Jamhuriyar Nijar sun shigar da kara a gaban kotu sun son a hukunta wadanda suka saci kudin jama'a a Nijar, a Najeriya kuwa kungiyar kasa da kasa ta tuntubar juna da sulhunta rigingimu ta bullo da tsarin koyawa sarakunan gargajiya a jihar Benue dubarun sulhunta al’umma