A cikin shirin za ku ji cewa masu garkuwa da jama'a don neman kudin fansa a Najeriya sun yi awon gaba da mutane 40 a yammacin jiya kan hanyar Kaduna zuwa Abuja, a yayinda malaman makarantun boko sun jingine aikin koyarwa a jamhuriyar Nijar bayan kisan gillar da wani dalibi ya yi wa malaminsa a jihar Tahoua.