A cikin shirin za a ji cewa a Najetriya hukumar EFCC ta kama tsohon gwamnan jihar Zamfara Abdul aziz Yari bisa zarginsa da handamar kudin kasa a yayin da hukumomi a kasar Gambiya suka bayyana fata na ganin an gurfanar da tsohon shugaban kasar Yahya Jameh a gaban kuliya bisa zarginsa da cin zarafin bil'Adama.