A cikin shirin za a ji cewa a Najeriya kamfanin jirgin sama na Emirate zai cigaba da jigilar fasinjoji bayan barazanar dena zuwa kasar daga wannan Alhamis, kana a wani mataki na ba wa al'umma damar cin gajiyar kiwon lafiya a Nijar, gwamnatin Damagaram ta bada gudummawar magunguna.