A cikin shirin za ku ji cewa, alkaluman da hukumar zaben Najeriya ta fitar na nuni da cewar matasan kasar ke kan gaba daga cikin jerin wadanda suka yi rijistar kada kur'a a babban zaben da ke tafe. A kasar Ghana tsarin inshorar lafiyar kasar ne ke fuskantar tazgaro tun bayan kaddamar da shi shekaru aru-aru da suka gabata.