1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Najeriya: Sabon fasali na dokar haraji

November 1, 2024

shirin sauya fasalin dokar karbar haraji a Najeriya na da burin sauyi kawo ci gaba, kasancewar kasar ta zaman ta baya ga dangi cikin batu na haraji.

https://p.dw.com/p/4mUst
NO FLASH Zentralbank von Nigeria
Hoto: public domain

 A karkashin shirin dai Abujar na fatan sauyin tsari na kasar tare da karkata zuwa ga harajin a cikin neman ginin kasa.To sai dai kuma tun  ba a kai ga ko'ina ba dai shirin na jawo kace-nace cikin kasar tare da jihohin arewacin kasar na nuna adawa da shirin da a cewarsu ke iya kai wa ga kara talauci a arewar.Atiku Bagudu dai na zaman ministan kasafin kudi da tsare-tsaren tattali na arzikin kasar.Babbar takadama cikin neman sauyin tsarin dai na zaman wani tanadi na haraji na mai saye.Tanadin kuma da ke  neman sauya harajin da ke zaman kusan kaso 30 cikin dari na daukacin kudin shiga na   jihohin.

Kafin yanzun dai harajin da ake karba a tudu da gangaren kasar ne dai ake rabashi cikin tarayyar Najeriya a tsakani na matakai na gwamnatin kasar uku.To sai dai kuma a karkashi na sabuwar dokar da tuni mahukuntan na Abuja suka mikawa majalisun kasar guda biyu, za a mayar da  harajin zuwa ga hedikwatocin manyan kamfanoinin da ke biyan na harajin. Abun kuma da a cewar Senata Bala Mohammed da ke zaman gwamnan Bauchi ke nufin jara ta'azzara ta talauci a cikin arewacin kasar da ke zaman na baya ga dangi. Tuni dai majalisun tarayyar guda biyu da suka Yi karatun farko bisa dokar suka dakatar har sai an tantance