A cikin shirin za ku ji a jihar Sokoto da ke Najeriya, manoma na ci gaba da kokawa kan wani tsohon bashi da suka karba a hannun gwamnatin tarayya, kuma suka kasa biya tsawon shekaru da suka gabata, inda suke rokon gwamnati da ta yafe masu wannan bashi.