A cikin shirin za a ji yadda sannu a hankali cutar zazzabin Lassa wacce aka sani da Lassa Fever, ke neman mamaye jihohin Najeriya, inda yanzu aka yi kiyasin ta bulla a jihohi 17 ciki har da Lagos babban birnin kasuwancin kasar. A Nijar kuwa barazanar matasan da ke komawa kasar daga Libiya ne ke shafar rayuwar mazauna yankin Agadez.