A cikin shiri za a ji cewa bayan da aka fara gangamin yakin neman zabe a Najeriya, wasu matasan arewacin kasar sun gana da shugabannin addinai da sarakunan gargajiya. Shugabannin kasashen Turai sun bazama a duniya don neman mafita kan dogaron da suke da makamashin Rasha tun bayan da ta soma yakin Ukraine.