A cikin shirin bayan labaran duniya akwai rahoto kan yadda jama'a a yankin Agadez na Jamhuriyar Nijar ke cewa ba sa ganin romon dimukuradiyya a yayin da kasar ke tunkarar babban zaben kasa da rahoto a kan yadda zaizayar kasa ke addabar mutanen Najeriya da rahoto a kan dakatar da dalibai mata masu juna biyu daga komawa makarantu a Laberiya.