A cikin shirin bayan labaran duniya za ku ji tattaunawar da DW ta yi da Fadar Shugaban Najeriya, inda gwamnati ke ba 'yan Najeriya hakuri a kan karuwar rashin tsaro a kasar, sai rahoto kan yadda ake cece-kuce a Nijar a kan kaddamar da sabbin jagororin kananan hukumomi. A Kamaru za ku ji yadda gwamnati ta yi kokarin dakile amfani da leda wurin sayar da dafaffen abinci.