A cikin shirin za a ji cewa a Najeriya dokar nan da majalisar dattawan kasar ta samar mai hukunta duk wanda aka kama ya biya masu garkuwa da jama'a kudin fansa na ci gaba da tayar da kura, a yayin da a Jamhuriyar Nijar a daidai lokacin da azumin watan Ramadana ke bankwana bukukuwan karamar Sallah ne ke hana wasu magidanda barci duba da yadda kayayaki suka yi tsada.