Bayan labaran duniya a cikin shirin za ku ji cewa an gudanar da bukukuwan karamar salla a cikin kwanciyar hankali duk da matsin tattlin arziki da ake fuskanta a wasu kasashen yammacin Afirka, a yayin da babban sakatare Janar na Majalisar Dinkin Duniya ya kai wata ziyarar aiki a wasu sansanonin 'yan gudun hijira a kasashen Najeriya da Nijar, duk a cikin shirin Afirka a Mako.