A cikin shirn za a ji cewa a daidai lokacin da ake cika shekara da kakaba dokar tabaci a wasu sassan kasar Kwango, wata cibiyar da ke nazari kan harkokin tsaro a Lardin Kivu ta sanar da cewa al'amurran tsaro sun kara sukurkucewa fiye da yadda ake tsammani, a yayin da Najeriya dokar hana zirga-zirga da babura da gwamnatin jihar Kaduna ta kaka na cigaba da tada kura.