A cikin shirin za a ji cewa a Najeriya al’amurra sun soma daidaita kamar yadda aka saba yau da kullum a jihar Sakkwato, bayan sassauta dokar hana fita ta sa’o’i 24 da gwamnan jihar ya kakaba., a daidai lokacin da wata sabuwar kungiyar 'yan bindiga ta bulla a jahar Rivers, bisa manufar fara tada hankali a sassan yankin Niger Delta.