A cikin shirin za a ji cewa A yayin da zaben Najeriya na 2023 ke kara karatowa 'yan takara daga jam'iyyar APC maimulki na kauracewa hada hotunansu na yakin neman zabe da Shugaba Muhammadu Buhari. A Jamhuriyar Nijar kuwa rashin cika alkawarin da Faransa take daukar masu, ya fara kai makura ga tsoffin sojojin da suka taya Faransar yakin duniya na biyu.