A cikin shirin za a ji cewa yaki da sauyin yanyi na fuskantar barazana a arewacin Najeriya, inda hauhawar farashin iskar gaz ya sa magidanta rungumar gawayi a matsayin makamashin girki a yayin da Shugaba Mohamad Bazoum na Jamhuriyar Nijar ya sha alwashin farfadowa tattalin arzikin yankin Agadez mai arzikin ma'adanin uranium.