A cikin shirin za aji cewa mahajjata daga sassa dabam-dabam na duniya suke hawan Arafa, mataki na biyu na kololuwar aikin hajji. A yayin da ma'aikata ke murnan biyan albashi a Jamhuriyar Nijar, 'yan kasuwar dabbobi sun tsawwala farashi domin cin kazamar riba. Hukumomi a Jihar Kano sun gano wasu makarantun kiwon lafiya na boge da ke horar da dalibai ba bisa ka'ida ba.