A cikin shirin za a ji tasirin ziyarar shugaban Amirka Joe Biden a yankin Gabas Ta Tsakiya. Majalisar Dinkin Duniya ta nuna fargabar cewa ga dukkan alamu Najeriya ba ta daga cikin kasashe da za su cimma muradun karni. Jam'iyyun siyasa a kasar Chadi na ci gaba da kai ruwa rana ga batun sake shata makomar kasar bayan mutuwar marigayi Idriss Daby.