A cikin shirin za a ji cewa A daidai lokacin da Shugaban Nijar Mohamed ya bukaci samun hadin kan alummar domin tinkarar matsalolin da kasar ke fama da su na tsaro, karin kudaden farashin man desil ko Gasoil da gwamnatinsa ta yi na ci gaba da tayar da kura, a najeriya kuwa gwamnati ta bukaci agajin kasashen waje don tinakrar matsalaolin tsaro da suka dabaibaiceta.