A cikin shirin za ku ji cewa a kasar Australiya kamar sauran kasashen duniya na zaman makoki a yayin da ake cigaba da alhinin rasuwar sarauniya Elizabeth ta II. Rashin tsaro da yawan amfani da kudi na haifar da damuwa a tarayyar Najeriya inda har ta kai ga cibiyar nazarin dimukurdiyya da ci gaban kasa ta CDD ta ce zai shafi babban zaben kasar da ke tafe.