A cikin shirin za ji cewa A Najeriya, jam'iyyar Labour ta Peter Obi na dada jan hankalin matasan duk da kalubale da take fuskanta. Gwamnatin Nijar ta soma nazarin samar da inshora da za ta kula da kawo sauki ga ambaliyar ruwa da ake fuskanta akai-akai. Fursunonin siyasa da aka sako a Masar na fuskantar tarin matsaloli ciki kuwa har da mayar da su saniyar ware da ake yi.