A cikin shirin za a ji cewa kasashen Afirka membobin kungiyar G5 Sahel sun tallata kokon baransu ga takwarorinsu masu hannu da shuni da su agaza masu yaki da ta'addanci. Hukumomi a jihar Sakkwato da ke tarayyar Najeriya sun shirya gasar rubuta tarhin daular Usmaniyya da aikin jihadin da Mujaddadi Shehu Usmanu Danfodiyo ya gabatar.