A cikin shirin za a ji cewa a yayin da zullumi da fargaba kan matsalolin rashin tsaro ke dada mamaye babban zaben Najeriya na 2023 da ke tunkarowa, kungiyoyin Fulani a kasar sun himmatu wajan bi ruga-ruga don tattaunawa da shugabannin al'umma. A Jamhuriyar Nijar gamayyar wasu likitocin kasar da suka yi karatun harhada magungunna ne suka gana da shugaba Mohamed Bazoum.