A cikin shirin za a ji cewa: A Najeriyar masana sun ce zai fi dacewa a rika tunanin maida da yan gudun hijira tushensu na asali. A Nijar, manoma na kokawa kan yadda wasu ke bin dare suna sace musu albarkatun gona. Mahukuntan a Chadi da Kamaru, sun ce dubban mutane sun rasa matsagunnasu sakamakon ambaliyar ruwa.