A cikin shirin za a ji cewa a Najeriya zargin badakalar fataucin miyagun kwayoyi da wata kotu a Amurka ke yiwa dan takarar jamiyyar APC Bola Ahmed Tinubu na ci gaba da tada kura a fagen siyasar kasar. Tsadar man fetur a Ghana ta sa 'yan majalisun dokokin kasar neman sahale masu aiki daga gida. Mata da matasa da ma gajiyayyu a Nijar ba sa cin moriyar arzikin da kasar ke samu in ji Rotab.