A cikin shirin za a ji cewa Ministar harkokin wajen Jamus Annalena Baerbock, ta ziyarci wasu al'ummomi a jihar Borno da ke yankin arewa maso gabashin Najeriya. Al'ummomi a karamar hukumar Maru ta jihar Zamfara da ke fama da matsalolin tsaro sun zargi jirgin sojojin Najeriya da jefa bam kan mutanen da su san hawa ba su san sauka ba.