A cikin shirin za a ji cewa a Najeriya wasu kungiyoyin da ke fafutikar alkinta muhalli sun zargi gwamnatocin yankin Kudu maso gabashin Kasar da yin marar hannu kan tallafin bala'o'i daga gwamnatin Najeriya. Matsalar tsaro da ke addabar sassan Najeriya ta sa gidajen haya da sauran filaye sun yi tashin gwabron zabi a manyan biranen kasar.