A cikin shirin za a ji cewa miliyoyin manoma a Jamhuriyar Nijar sun karkata zuwa ga noman rani samakon yadda damina ke zo masu da gardama. A yayin da ake dab da zaben gwamnoni a Najeriya wasu jam’iyyun siyasa sun kaddamar da taron wayar da kan magoya bayansu yadda za a gudanar da jifar kuri’a da dakon sakamakon zabe.