1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

EU: Shirin samarwa Afirka riga-kafin corona

Suleiman Babayo RGB
September 15, 2021

Kungiyar EU na son ganin an samar da maganin cutar Covid-19 ga kasashe masu tasowa gami da tallafi ga kasar Afghanistan wadda take tsaka mai wuya kan ayyukan jinkai. 

https://p.dw.com/p/40M5B
Frankreich | Ursula von der Leyen spricht im EU Parlament
Hoto: Yves Herman/REUTERS

Shugabar Hukumar Kungiyar Tarayyar Turai ta yi jawabi ga majalisar dokokin kungiyar inda ta mayar da hankali kan batutuwa da suka shafi samar da maganin cutar Covid-19  ga kasashe masu tasowa musamman na Afirka gami da tallafi ga kasar Afghanistan wadda take tsaka mai wuya kan ayyukan jinkai. 

Yayin jawabin, shugabar hukumar ta Tarayyar Turai Ursula von der Leyen ta nuna aniyar kungiyar na samar da riga-kafin cutar ta coronavirus kimanin miliyan 200 ga kasashe masu tasowa, kuma jawabin na wannan Laraba ke zama jawabinta na biyu tun lokacin da ta karbi ragamar tafiyar da kungiyar. Sannan ta kara da cewa:

"Tawagar Turai ta zuba jarin kimanin kudin Euro miliyan dubu domin samar da karfin yin riga-kafin a Afirka. Mun kuma samar da magungunan riga-kafi miliyan 250 da muka raba da sauran kasashen duniya. Zan bayyana yau cewa hukumar Tarayyar Turai ta kara gudumawar riga-kafin miliyan 200 har zuwa tsakiyar wannan shekara."

Game da halin da ake ciki a kasar Afghanistan, hukumar ta ce, tana shirye da taimakon da ya dace domin dakile yiwuwar samun tabarbarewar ayyukan jinkai. Ursala von der Leyen ta ce tana tare da mutanen Afghanistan musamman mata da yara gami da 'yan jarida da suke fuskantar tsangwama karkashin Kungiyar Taliban  da ta kwace madafun ikon kasar.

Dubban mutane ne suka tsere daga kasar ta Afghanistan tun lokacin da Taliban ta shiga birnin Kabul fadar gwamnatin kasar. Kuma yanzu hukumar ta Tarayyar Turai karkashin shugabancin Ursala von der Leyen, tana iya kokarinta domin dakile matsalolin jinkai a kasar ta Afghanistan.