A cikin shirin za ku ji cewa kungiyoyin fararen hula a Nijar sun zargi gwamnatin kasar da zama 'yar koran kamfanonin kasashen ketare masu aikin hakar ma'adinan karkashin kasa, sakamakon wata dokar da ke shirin rage kudin harajin da take karba da ta shigar a gaban majalisa.