A cikin shirin za a ji cewa a yayin da aka tafka wani ruwan sama kamar da bakin kwarya a yankin Damagaram, hukumar kwana-kwana ta tabbatar da samun mumunar ambaliya a nan gaba. Ruwan sama mai karfi ya haifar da ambaliyar ruwa a jihohin Arewa maso gabashin Najeriya inda ya raba mutane da gidajen su tare da raba hanyar Gombe Zuwa Bauchi.