A cikin shirin za a ji cewa a Jamhuriyar kungiyoyin agaji sun bi sahun takwarorinsu na raya ranar ma’aikatan agaji ta duniya wacce Majalisar Dinkin Duniya ta kaddamar a shekara ta 2008 domin tunawa da jami’an agaji. A Najeriya hukumar da ke sa ido a kan kafofin yada labaru ta soke lasisin wasu gidajen rediyo da telbishi har guda 52 a kasar, matakin da wasu ke alakantashi da siyasa.