A cikin shirin za a ji a yayin da matsalar tsaro ke kara tabarbarewa a arewacin Najeriya an kammala wani taron dattawa da kwararru a bangaren tsaro domin tattauna hanyoyin magance wannan matsalar. A Jamhuriyar Nijar kuwa hukumar zabe mai zaman kanta ta kasar ce ke shirin soma aikin rijistar yan kasar mazauna ketare kan batun zaben cike gurbi.