A cikin shirin za a ji cewa kungiyar ASUU ta janye yajin aikin da ta shafe sama da watanni 8 ta nayi bayan wata tattaunawa da masu fada a ji. A jamhuriyar Nijar kuwa ofishin ministan harkokin wajen kasar ne yayi amfani da kungiyoyin farar hula domin wayar da kawunan al'umma kan yancinsu na shige da fice.